Saturday, June 25, 2022

DAVIDO YABA DA TALLAFIN KARATU

 


Wani matashi dan kasar Ghana mai suna Suleiman Morro, ya dauki hankulan mutane a lokacin da aka raba sakamakon jarabawar sa ta West African Examinations Council (WAEC) ta yanar gizo. haziki Sulaiman ya samu A1 guda Tara a jarabawarsa amma saboda rashin kudi da iyayensa ke da shi don daukar nauyin karatunsa a matakin jami'a yasa ya zauna agida ba-cas-ba-as.

Davido cikin farin ciki ya sanar da cewa ya sami damar gano yaron kuma ya dauki niyyar tallafa masa. An bai wa dalibin dan kasar Ghana tallafin karatu a makarantar mahaifin Davido ta Adeleke University, ya karanci duk abinda zai karanta ko shekara nawa ne. 

Mawakin ya kuma kara da cewa yaron zai samu wasu ababen more rayuwa kamar masauki da alawus duk tsawon karatunsa. David Adedeji Adeleke wanda aka fi sani da Davido, mawaki ne a Nigeria da ne awajern hamshakin mai kudinnan Adeleke.Anhaife Davido a ranar 21 ga Nuwamba, 1992).



1 comment:

  1. Davido kuma to ina su M sharif da Breaker kunfi shi iya waka yafi ku iya kyauta

    ReplyDelete

KOYI FOREX CIKIN SAUKI (2)