Saturday, June 25, 2022

DUK BUDURWAR DA TA NUNA MAKA HALI 3 TANA KAUNARKA




Duk macen da take sonka tabbas zata ringa nuna wasu dabi'u a duk lokacin da take kusa da kai, ya rage gareka ka lura da wadannan dabi'un, wasu daga cikinsu sune;


 1---KULAWA- Duk budurwar dake so da kaunarka zata ringa nuna damuwarta da kulawa dakai ta hanyar lura da al'amuranka na yau da kullum. Wani lokacin ma takan yi tambaya, Misali

Ka ci abinci kuwa?

Me kafi so arayuwarka?

Da dai sauran irin wadannan tambayoyi.

Hakanna zata ringa nuna kishinka musamman ga 'yan mata kawayenta.

2---BURGEWA - Duk yarinyar da take sonka sosai za ta ringa kokarin burge ka. Don haka ne idan wani abu yafaru za ta so ka zama mutum na farko da ya fara gani ko jin abun daga gareta.

Ko kwalliya ta yi tafi so ka fara gani, wannan ne ma yasa wasu yan matan sai sufita bayan sun yi kwalliyar su bi hanyar da suka san kana nan su wuce, idan kuwa tasan baza ka ganta ba, za ta yi kokarin wuce wa ta inda abokanka suke zama, sun san sakon zai je. 

Bugu-da-kar, idan tana da wayar hannu za ta yi ta daukar hoto dan ta nuna maka kawai dan ta birge ka. Wasu in sunyi hotunan sukan iya turawa ababan kaunar nasu wasu ko kuwa basa iya turawa.

3---HALI - Budrwar da ke hakikanin kaunarka akowane lokaci zata ringa kokarin nuna kyawawan halaye agabanka tahanyar gyara kalamanta,sabon salon murmushi, saitwa da gyara tafiyarta koda kuwa hakan ba halayenta bane,kai koda halayenta ne sai ta dan sauya ko kadanne.

Maza ma ba'abarsu abayaba wajen kokarin nuna irin wadannan halaye ga wadanada suke so Kuma suke kauna. 

Shin kin taba nunawa saurayinki daya daga cikin wadannan halaye?

Lokacin da kaga ta nuna maka irin wadannan halaye wane martani ka mayar mata dashi?

Za ka/ki iya bayyana wani abu da aka fuskanta a rayuwar soyayya a sashin sharhi wtao(comment)


1 comment:

KOYI FOREX CIKIN SAUKI (2)