Kasar Da Aka Umarci Maza Da Su Auri Mata Biyar Ko Kuma Su Fuskanta Gidan Yari
Mafarkin mafi yawan mata shine su hadu da wani mutum wanda shi ne zai zama jigon rayuwarsu don jin daÉ—in rayuwa ba tare da tsangwama ba. Wannan baya yuwuwa kai tsaye sai ta hanyar auratayya, wanda aure a halin yanzu ya zama kamar kayan gabas, saboda wahalhalun da ke kunshe dashi. Auren mace daya kenana ballantana ace mutum ya auri biyu ko sama da haka.
Acewar rahotanni da dama, Sarkin Swaziland, Sarki Mswati III shekaru uku da suka gabata a watan Yunin 2019 ya ba da sanarwar cewa maza su auri akalla mata biyar ko fiye ko kuma su fuskanci hukuncin dauri.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Eswatini, IHarare, ana bukatar mazaje a Swaziland su auri mata da yawa domin kowace mace ta samu miji.
Sarkin ya bayyana cewa akwai mata fiye da maza a kasar Swaziland wanda a cewar sarkin babbar matsala ce ga kasar idan yazama ga maza ga mata tuli amma mazan sun gaza aure matan.
Wannan ra'ayi na sarkin ya sha suka daga bangarori da dama.
Shi kansa Sarki Mswati yana da mata 15 da ’ya’ya 36,yayin da mahaifinsa ke da mata sama da 70 da ‘ya’ya sama da 150. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sarki Mswati ya yi kira ga dukkan mazan kasar da su auri akalla mata biyar kuma gwamnati ta tabbatar wa mazajen cewa za ta biya kudin daurin auren tare da siya musu gidaje.
Sarki Mswati ya yi gargadin cewa duk mace ko namiji da suka yi adawa da shawarar "za su fuskanci hukuncin daurin rai da rai".
.jpeg)
No comments:
Post a Comment