Monday, July 4, 2022

KOYI FOREX CIKIN SAUKI

 MENENE FOREX TRADING 

Forex trading  kasuwanci ne da ake hada- hadar kudaden ta duniya ta hanyar chanji.

Yadda ake shi wannan kasuwanci ana gudanar dashine gaba dayan shi ayanar gizo-gizo wato Internet ana iya amfani da wayar hannu da kuma computer  wajan gudanar da wannan kasuwanci. 

Akasuwar forex kanada damar siya ko siyar da kowane irin kudi na kowace kasa a fadin duniya ta hanyar broker. 

WANENE BROKER?

Broker kamfanine ne da yake da asusu a wannan kasuwar ta forex ganin yadda kasuwar forex tayi tsauri akan kananun yan kasuwar chanji, kasancewar sai kanada manyan-manyan takardun shaida na gwamnati tare da makudan kudade zaka iya siye da siyarwa awannan kasuwa.

To wannan ne yasa da yawa daga cikin kananun yan kasuwar chanji basa iya gudanar da wannan kasuwancin da farko.  Wannan ne yasa wasu daga cikinsu suka hada gwiwa suka mallaki dukkan abinda ake bukata na takardun shaida da kudaden da ake bukata dan bawa kananun yan kasuwa kamar ni da kai damar shiga wannan kasuwa dan gudanar da kasuwanci da kananan kudade ta hanyar abinda ake kira leverage.


Idan kana da tambaya akan abinda aka gabatar asama sai kayi a sashin sharhi wato comment


Zamu ci gaba...

2 comments:

KOYI FOREX CIKIN SAUKI (2)