Saturday, June 25, 2022

FARFESA SOYINKA YA RASU

Farfesa Femi Soyinka, Farfesa a fannin ilimin fata, Venereology da Clinical Immunology, ya rasu. 

FEMI SOYINKA


Kanine ga fitaccen marubucin wasan kwaikwayo kuma bakar fata na farko a Afirka, Farfesa Wole Soyinka.

Acewar wata sanarwa daga iyalan Soyinka na Ake/Isara, jihar Ogun, Farfesa Soyinka ya rasu ne a safiyar ranar Talata, 14 ga watan Yuni, 2022. Ya rasu yana da shekara 85 a gidansa dake kauyen Kukumada, Ibadan, jihar Oyo. Sanarwar ta samu sa hannun dansa, Ayodele a madadin iyalansa.

An haife shi a shekara ta 1937, Farfesa Femi Soyinka ya sami digiri na likita a fannin likitanci da tiyata MBChB daga Jami'ar Heidelberg, a 1964; kuma ya yi digiri na Doctor of Medicine (MD) duk daga jami'a guda a 1965. Ya kware kuma ya yi aiki a matsayin likitan fata, Venereologist da Allergologist a Jami'ar Giessen, a 1969.

A cikin 1972, ya sami digiri na biyu na Kiwon Lafiyar Jama'a daga Makarantar Kiwon Lafiya ta Hadassah, (MPH) Isra'ila.

Bayan haka, ya bayar da gudunmawa sosai wajen gina kungiyoyin akasashen waje a duk shiyyoyin siyasar Nijeriya shida ta hannun wata kungiya mai zaman kanta mai New Initiative for the Enhancement of Life and Health (NELAH) da aka fi sani da; Cibiyar sadarwa akan Da'a/Hakkin Dan Adam, Doka, Rigakafin HIV/AIDS, Tallafawa da Kulawa (NELA). 

Ya taba zama shugaban kungiyar da ke kula da cutar kanjamau a Afirka kuma ya samu nasarar gudanar da taron kasa da kasa kan cutar kanjamau da STIs a Afirka (ICASA) a Abuja, Najeriya a shekara ta 2005.Ya rasu ya bar mata, ‘ya’yansa, jikoki da jikoki.

Sanarwar ta kara da cewa, dangin za su sanar da shirye-shiryen binnewa daga baya.

DAVIDO YABA DA TALLAFIN KARATU

 


Wani matashi dan kasar Ghana mai suna Suleiman Morro, ya dauki hankulan mutane a lokacin da aka raba sakamakon jarabawar sa ta West African Examinations Council (WAEC) ta yanar gizo. haziki Sulaiman ya samu A1 guda Tara a jarabawarsa amma saboda rashin kudi da iyayensa ke da shi don daukar nauyin karatunsa a matakin jami'a yasa ya zauna agida ba-cas-ba-as.

Davido cikin farin ciki ya sanar da cewa ya sami damar gano yaron kuma ya dauki niyyar tallafa masa. An bai wa dalibin dan kasar Ghana tallafin karatu a makarantar mahaifin Davido ta Adeleke University, ya karanci duk abinda zai karanta ko shekara nawa ne. 

Mawakin ya kuma kara da cewa yaron zai samu wasu ababen more rayuwa kamar masauki da alawus duk tsawon karatunsa. David Adedeji Adeleke wanda aka fi sani da Davido, mawaki ne a Nigeria da ne awajern hamshakin mai kudinnan Adeleke.Anhaife Davido a ranar 21 ga Nuwamba, 1992).



DUK BUDURWAR DA TA NUNA MAKA HALI 3 TANA KAUNARKA




Duk macen da take sonka tabbas zata ringa nuna wasu dabi'u a duk lokacin da take kusa da kai, ya rage gareka ka lura da wadannan dabi'un, wasu daga cikinsu sune;


 1---KULAWA- Duk budurwar dake so da kaunarka zata ringa nuna damuwarta da kulawa dakai ta hanyar lura da al'amuranka na yau da kullum. Wani lokacin ma takan yi tambaya, Misali

Ka ci abinci kuwa?

Me kafi so arayuwarka?

Da dai sauran irin wadannan tambayoyi.

Hakanna zata ringa nuna kishinka musamman ga 'yan mata kawayenta.

2---BURGEWA - Duk yarinyar da take sonka sosai za ta ringa kokarin burge ka. Don haka ne idan wani abu yafaru za ta so ka zama mutum na farko da ya fara gani ko jin abun daga gareta.

Ko kwalliya ta yi tafi so ka fara gani, wannan ne ma yasa wasu yan matan sai sufita bayan sun yi kwalliyar su bi hanyar da suka san kana nan su wuce, idan kuwa tasan baza ka ganta ba, za ta yi kokarin wuce wa ta inda abokanka suke zama, sun san sakon zai je. 

Bugu-da-kar, idan tana da wayar hannu za ta yi ta daukar hoto dan ta nuna maka kawai dan ta birge ka. Wasu in sunyi hotunan sukan iya turawa ababan kaunar nasu wasu ko kuwa basa iya turawa.

3---HALI - Budrwar da ke hakikanin kaunarka akowane lokaci zata ringa kokarin nuna kyawawan halaye agabanka tahanyar gyara kalamanta,sabon salon murmushi, saitwa da gyara tafiyarta koda kuwa hakan ba halayenta bane,kai koda halayenta ne sai ta dan sauya ko kadanne.

Maza ma ba'abarsu abayaba wajen kokarin nuna irin wadannan halaye ga wadanada suke so Kuma suke kauna. 

Shin kin taba nunawa saurayinki daya daga cikin wadannan halaye?

Lokacin da kaga ta nuna maka irin wadannan halaye wane martani ka mayar mata dashi?

Za ka/ki iya bayyana wani abu da aka fuskanta a rayuwar soyayya a sashin sharhi wtao(comment)


Friday, June 24, 2022

KO TA YAYA YA SAMU RIBA ADADIN DUKIYAR DANGOTE A AWANNI

 Elon Musk babban attajirin Nan ya samar  da jimillar tattalin arzikin Aliko Dangote A Cikin Sa'o'i 8, yayin da attajirin Najeriya ya yi asarar N105.33bn.

Elon Musk ya ci gaba da nuna cewa shi sarkin masu kudi ne yayin da ya samu jimillar dukiyar Aliko Dangote a cikin ‘yan sa’o’i kadan Tattalin arzikin Musk na zuwa ne a daidai lokacin da kamfaninsa na lantarki na Tesla ya sanar da samun karin riba bayan cinikin Dangote a ranar Talata.

A ranar Talata, Yuni 21, 2022, bayanai daga


masu sa ido na Forbes sun nuna cewa Elon Musk a cikin sa'o'in 8 a Amurka ya samu Naira tiriliyan 6.10 (dala biliyan 14.5).

KA AURI MATA BIYAR KO KAJE GIDAN YARI



Kasar Da Aka Umarci Maza Da Su Auri Mata Biyar Ko Kuma Su Fuskanta Gidan Yari

Mafarkin mafi yawan mata shine su hadu da wani mutum wanda shi ne zai zama jigon rayuwarsu don jin daÉ—in rayuwa ba tare da tsangwama ba. Wannan baya yuwuwa kai tsaye sai ta hanyar auratayya, wanda aure a halin yanzu ya zama kamar kayan gabas, saboda wahalhalun da ke kunshe dashi. Auren mace daya kenana ballantana ace mutum ya auri biyu ko sama da haka.

Acewar rahotanni da dama, Sarkin Swaziland, Sarki Mswati III shekaru uku da suka gabata a watan Yunin 2019 ya ba da sanarwar cewa maza su auri akalla mata biyar ko fiye ko kuma su fuskanci hukuncin dauri. 

A cewar kamfanin dillancin labarai na Eswatini, IHarare, ana bukatar mazaje a Swaziland su auri mata da yawa domin kowace mace ta samu miji.

Sarkin ya bayyana cewa akwai mata fiye da maza a kasar Swaziland wanda a cewar sarkin babbar matsala ce ga kasar idan yazama ga maza ga mata tuli amma mazan sun gaza aure matan. 

Wannan ra'ayi na sarkin ya sha suka daga bangarori da dama.

Shi kansa Sarki Mswati yana da mata 15 da ’ya’ya 36,yayin da mahaifinsa ke da mata sama da 70 da ‘ya’ya sama da 150. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sarki Mswati ya yi kira ga dukkan mazan kasar da su auri akalla mata biyar kuma gwamnati ta tabbatar wa mazajen cewa za ta biya kudin daurin auren tare da siya musu gidaje.

Sarki Mswati ya yi gargadin cewa duk mace ko namiji da suka yi adawa da shawarar "za su fuskanci hukuncin daurin rai da rai".

Monday, June 20, 2022

TALLAFIN KARATU (SCHOLARSHIP)

 Ilimi akowane zamani shi ne kashin bayan cigaba a siyasa da tattalin arziki kai harma da duk sauran bangarori na rayuwa. Akan haka ne makarantar New Jersey Institute of Technology isdake Amurka suka bude shafin su na yanar gizo-gizo don tallafawa masu karamin kafi amma kuma masu kokari da hazaka. Idan kana bukatar shiga sai ka shiga wannnan link don Karin bayani da kuma cike fom.

https://scholarship-positions.com/merit-scholarships-for-international-students-at-new-jersey-institute-of-technology-usa/2021/06/17/


Idan kana bukatar sanin wasu kasashen dake bada tallafin karatu(SCHOLARSHIP) to se kasa sunan kasar a comment

BASHIN BANKI BA TARE DA JINGINAR DA KOMAI NAKA BA


 Shekaru da suka shude idan aka ce bashin banki, abinda ke zuwa ran mutum shine jingina (collateral). To yanzu zamani ya Kara sauyawa, domin akwai bankuna wadanda yanzu za ka iya rance ba tare da jingina ba. Kawai abinda kake bukata, ka cike yan sharudda da ka'idoji. Bankunan da ke bada bashi ba tare da jinginar da komai naka ba sun hada da;

1- FIRST BANK

2-WEMA BANK

3-STANBIC IBTC

4- ZENITH BANK

5- FIDALITY

6-UBA
   
Wadannan sune wasu daga cikin bankunan da suke bada bashi ba tare da jinginar da komai ba.
Idan kana son sanin banki ka suna bayarwa ko a'a to ka rubuta sunan bankin da kake da shi a comment.




KOYI FOREX CIKIN SAUKI (2)