![]() |
Albasa na da matukar amfani a rayuwar mu ta yau da kullum haka ne yasa masana suka yi kykyawan bincike akanta. Ga kadan daga cikin amfaninta.
Albasa na taimakawa wajen inganta lafiyar zuciya. Acikin albasa akwai sinadarin flavonoids da thiosulfinates. Me waɗannan sinadarai suke yi ajikin mutum? flavonoids a cikin albasa yana taimakawa wajen rage mummunan cholesterol a cikin jiki. kuma shi thiosulfinates Yana taimakawa wajen daidaita jini. Albasa tana da amfani wajen rage haɗarin bugun zuciya da bugun jini.
Bugu da Kari albasa na maganin sanyi ko wane iri, ta hanyar cinta danya a abinci ba tare da an dafa ba.
.jpeg)
No comments:
Post a Comment