Saturday, June 18, 2022

MASU KUDIN DUNIYA

 

1. Elon Musk 

Shekaru: 50 

Ƙasa: Afirka ta Kudu 

Kamfanoni: Tesla, SpaceX, The Boring Company, Neuralink, Twitter, PayPal 

Darajar Dukiya $265.4 biliyan 

Masana'antu: Fasahar Motoci Elon Musk shine mutum mafi arziki a duniya kuma ya tara yawancin dukiyarsa bayan ya kafa Tesla Wanda ya bayyana cewa za a iya siyayya a kafaninsa da kudin fasahar zamani wato crypto currency.


2. Bernard Arnault

Shekaru: 73 

Ƙasa: Faransa 

Kamfanin: LVMH 

Darajar Dukiya: $151.1 biliyan 

BernardArnault ya tara dukiyarsa a cikin masana'antar kayan alatu tare da mallakar fitattun samfuran duniya irin su Louis Vuitton da Christian Dior. Arnault kuma ya mallaki otal-otal na alfarma da layukan jirgin ruwa waɗanda kawai suka ƙara masa arzikinsa tsawon shekaru.

3. Jeff Bezos 

Shekaru: 58 

Ƙasa: Amurka 

Kamfanin: Amazon

 Darajar Dukiya: $151.8 biliyan 

Masana'antu: kasuwancin yanar gizo-gizo da Fasaha Yana da shekaru 30, Jeff Bezos ya bar masana'antar hada-hadar kudi don fara kasuwancin littattafai akan yanar gizo-gizo. kamfanin Amazon nasa ne, kuma a halin yanzu yana da darajar sama da dala tiriliyan 1. Bezos ne yake jagorancin fagen kasuwancin e-commerce, wanda ya zama ɗaya daga cikin manyan masana'antu a duniya.



No comments:

Post a Comment

KOYI FOREX CIKIN SAUKI (2)