BTC ya faɗi ƙasa da $19k yayin da yake haɓaka asarar masu hannun jarinsa.
A ranar 18 ga Yuni, farashin Bitcoin (BTC) ya faɗi ƙasa da dala 20,000, mafi girman tarihin faduwa da ya kai a cikin 2017 kuma mafi ƙanƙanta darajar da ta ragu tun Disamba 2020.
Wannan ya zo a daidai lokacin da kasuwar crypto take neman farfadowa daga dogon suman da tayi.
A halin yanzu, Bitcoin darajarsa na kan $19,081 bayan ya kai $19,000 na ɗan lokaci kuma yana iya kaiwa ƙasa da $18,926 kafin ya sake komawa sama. Bitcoin yanzu ya ragu da 9.00% a rana daya, ya Kuma fadi da 34.47% a cikin kwanaki bakwai da suka gabata.
Bugu da ƙari kuma, haɗarin yana nufin cewa Bitcoin ya yi asarar kusan dala biliyan 40 daga kasuwar sa a cikin sa'o'i 24 yayin da ya yi kasa daga dala biliyan 402 na jarinsa zuwa dala biliyan 363 a wannan lokacin.

No comments:
Post a Comment